Skip to content

Bambancin rubutun fim da littafi

Banbancin rubutun fim da littafi

Bambancin Rubutun Fim da Littafi: Abubuwan da Marubuci Yahaya Sani Kaya Ya Bayyana

Jamilu Abdulrahman (Haiman Raess) ne ya jagoranci gabatar da wannan tattaunawar a cikin shirin Kaifin Alƙalami na Bakandamiya Reading Club a ranar 25 ga watan Agusta na 2024. Mun tattara muku shi cikin makala kamar haka:

Gabatarwa

Rubutun fim da rubutun littafi duk hanyoyi ne na ƙirƙirar labari da isar da saƙo, amma kowannensu yana da nasa tsari da salon rubutu. Marubucin da yake rubuta littafi yana da damar yin amfani da kalmomi wajen bayyana tunani, yanayi da abubuwan da ba lallai ne a iya nunawa a zahiri ba. Shi kuwa marubucin fim, dole ne ya riƙa la’akari da yadda abin da ya rubuta zai kasance idan aka kai shi wajen aiwatar da shi.

A yayin shirin Kaifin Alƙalami na Bakandamiya Reading Club, an tattauna batun “Bambancin Rubutun Fim da Littafi” tare da marubucin fina-finan Hausa, Yahaya Sani Kaya, wanda ya yi bayani dalla-dalla kan bambancin rubutun fim da na littafi, matakan rubuta screenplay, ƙalubalen da marubutan fim ke fuskanta, da kuma shawarwarin da yake ba masu sha’awar shiga wannan fanni.

Rubutun fim da rubutun littafi

Yahaya Sani Kaya ya kwatanta rubutun fim da na littafi da zanen gida da gininsa. A cewarsa, a zane mutum na iya tsara abubuwa da dama, amma ba lallai ne duk abin da aka tsara a zane ya kasance mai yiwuwa a gini ba.

Ya ce rubutun fim yana nufin aikatawa, don haka dole marubuci ya rubuta abin da zai iya yiwuwa a zahiri. Wannan ya bambanta da littafi, inda marubuci yake da faɗin dama wajen yin bayani da amfani da kalmomi yadda yake so, ko da abin da yake bayani a kansa ba zai yuwu a duniyar zahiri ba.

Ya kawo misali da cewa, a rubutun littafi marubuci zai iya cewa:

“Saboda farin Gimbiya Falisha har jinin da ke yawo a jikinta ana gani.”

Amma a fim, irin wannan bayanin ba zai kasance mai sauƙin aiwatarwa ba, domin babu yadda za a samu jarumar da za a riƙa ganin jinin da ke yawo a jikinta kai tsaye.

Matakan rubuta fim

A cewar Yahaya Sani Kaya, rubutun fim yana da wasu tsare-tsare da matakai da marubuci yake buƙatar bi. Daga cikin waɗannan matakai akwai:

1. Fitar da idea: Wannan shi ne matakin samun tunanin da za a gina rubutun fim a kansa.

2. Synopsis: Bayan fitar da idea sai a samar da synopsis, wato taƙaitaccen labarin da aka tsara shi cikin salon da zai iya fisgar zuciyar mai karatu, ko kuma ya sa Producer ya yi azarbabin mallakar labarin.

3. Brainstorming: Wannan shi ne matakin shigo da wasu abubuwa domin labarin ya sake zama a taƙaice, a tantance shi kuma a tankade shi. Ya ce wannan ya fi faruwa idan rubutun haɗaka ne.

4. Blocking: Wannan shi ne matakin da marubuci yake tsara duk fitowar abubuwan da za su faru a cikin labarin.

5. Characterisation: A rubutun fim, marubuci dole ya riƙa tafiya bisa halayen jaruman da ya gina, domin gudun kada ya sauke jarumansa daga turbar da ya fara dasu ba tare da wani dalili ba.

Faɗin bayani a rubutun littafi

Ya bayyana cewa rubutun littafi, wanda ake kira rubutun zube, rubutu ne da ake yin sa ta hanyar ba da labari, inda marubuci yake da damar yin amfani da kalmomi wajen ƙawata bayaninsa.

A cewarsa, marubucin littafi zai iya yin wani bayani mai zurfi ko amfani da kwatanci wanda ba zai yiwu a nuna shi a fim ba. Wannan shi ne ɗaya daga cikin abubuwan da suka bambanta rubutun littafi da rubutun fim.

Shawara ga masu sha’awar rubutun fim

Yahaya Sani Kaya ya shawarci masu sha’awar rubutun fim da su nemi ilimi a kan duk wani abu da ba su sani ba. Ya ce ya kamata su dage wajen kwatantawa har su kware.

A cewarsa, kafin mutum ya fara rubutun fim, dole ya nemi ilimin rubutun fim, domin babu abin da ake fara shi da ka kawai sannan a yi tsammanin za a dace.

Fina-finan da ya rubuta

Yahaya Sani Kaya ya bayyana cewa ya rubuta fina-finai da yawa, waɗanda a kiyasi za su kai kusan 20. Wasu daga cikin fina-finan shi kaɗai ya rubuta, yayin da wasu kuma ya yi haɗaka da wasu marubuta.

Daga cikin waɗanda ya ambata waɗanda suka shiga kasuwa akwai:

  1. 1. Mai Unguwa
    2. Da Ban Ganta Ba
    3. Sirrin Boye
    4. Yahoo Boy
    5. Dafin Zuciya
    6. Zuciya
    7. Alhaki
    8. Agolan Kauye
    9. Da sauransu.

Alaƙar marubutan fim da daraktoci

Ya bayyana cewa alaƙar marubucin fim da sauran masu ruwa da tsaki a masana’antar tana iya bambanta daga mutum zuwa mutum.

A cewarsa, wani lokaci marubutan fim suna samun matsala da Darakta musamman idan suka ga an canja wani abu daga abin da suka rubuta.

Ya ce yadda ake ɗaukar marubuci a masana’antar fina-finan Hausa ya danganta da wanda yake ɗaukar marubucin da kuma yadda yake kallon aikin marubucin.

Matsalar biyan haƙƙin marubuci

Dangane da batun biyan haƙƙin marubuci, Yahaya Sani Kaya ya bayyana cewa Executive Producer shi ne mai fim, kuma shi ne wanda zai biya marubuci kuɗin aikinsa.

Sai dai ya ce wani lokaci marubuci na iya kammala aiki amma ya gagara samun kuɗinsa cikin sauƙi. Ya kwatanta hakan da sauran harkokin kasuwanci, inda mutum zai iya kammala aiki amma ya fuskanci matsalar cika masa abin da aka yi masa alkawari.

Sai dai ya jaddada cewa hakan ya danganta da wanda ya ba mutum aikin, domin akwai waɗanda ba sa samun matsala wajen biyan haƙƙin aiki.

Inda za a koyi rubutun fim

Yahaya Sani Kaya ya bayyana cewa akwai makarantu na online da ake koyar da rubutun fim. Ya ce shi ma yana da irin wannan makaranta da ake gudanar da karatu ta WhatsApp, kuma ya riga ya yaye ɗalibai sau biyu.

Ya bayyana cewa sunan makarantar shi ne Screenplay For Beginners.

Matakin shiga makarantar kuwa shi ne:

1. Yin registration.
2. Saka ɗalibin cikin group ɗin karatu.

Ya ce duk wanda yake da sha’awar shiga zai iya tuntuɓarsa ta private.

Shin ana samar wa ɗalibai aiki bayan kammala karatu?

Da aka tambaye shi ko ana samar wa ɗaliban da suka kammala karatu wata dama ta shiga aikin rubutun fim, Yahaya Sani Kaya ya bayyana cewa samun ilimi ba lallai ne ya zama tabbacin samun aiki ba.

Ya kwatanta hakan da karatu, inda mutum zai iya yin karatu ba tare da an tabbatar masa da cewa zai samu aiki ba. Sai dai ya ce ilimi yana da amfani, domin idan mutum ya koya kuma ya iya kamar yadda ake fata, zai iya amfani da wannan ƙwarewa idan dama ta samu.

Ya kuma bayyana cewa idan wani aiki ya zo ta bangarensa, yana ƙoƙarin janyo mutane. Idan aiki ya yi masa yawa, ko kuma aka kawo masa ƙaramin aiki da ba zai iya yi da kuɗin da aka bayar ba, sai ya ba da shawarar ɗaya daga cikin ɗalibansa domin ya samu aikin.

Bambancin marubutan fim na arewa da na kudu

Dangane da bambancin masu rubutun fim na Arewa da na Kudu, Yahaya Sani Kaya ya bayyana cewa babban bambancin shi ne yadda ake ba marubuta muhimmanci a masana’antun biyu.

A cewarsa, a masana’antar Kudu ana ɗaukar marubuta da muhimmanci, sabanin yadda yake gani a masana’antar Arewa, inda ake iya kallon marubuci kamar ba kowa ba.

Ya kuma ce wani lokaci Producers na Arewa ba sa ba marubuta damar rubuta abin da suke ganin zai yi kyau, sai dai abin da suke so. A cewarsa, hakan yana taimakawa wajen rage armashin labarin.

Ya ƙara da cewa a yanzu wasu masu shirya fim suna kawo idea ga marubuci ne su nemi ya buɗa musu ita, yayin da daidaikun mutane ne suke barin marubuci ya kawo musu nasa idea.

Ƙalubalen da masu son rubutun fim za su fuskanta

A cewar Yahaya Sani Kaya, ɗaya daga cikin matakai mafi wahala shi ne juriya wajen koyo.

Ya ce wasu mutane suna saurin sarewa musamman idan suka ga kamar ba sa ganewa. Saboda haka, mai son koyon rubutun fim yana buƙatar juriya da jajircewa.

Ya kuma ba da shawarar cewa idan hali ya ba mutum dama, ya mallaki laptop, domin hakan zai taimaka masa wajen koyon da kuma gudanar da aikin rubutun fim.

Kammalawa

Bayanin Yahaya Sani Kaya ya nuna cewa rubutun fim yana da bambanci da rubutun littafi, musamman wajen yadda marubuci yake tsara abin da zai faru da kuma yadda za a iya aiwatar da shi a zahiri. Yayin da marubucin littafi yake da faɗin dama wajen yin bayaninsa ta hanyar kalmomi, marubucin fim yana buƙatar la’akari da abin da za a iya gani da kuma aikatawa.

A ƙarshe, babban darasin da ya fito daga tattaunawar shi ne muhimmancin neman ilimi, juriya da ƙwarewa ga duk mai son shiga fannin rubutun fim. Kamar yadda Yahaya Sani Kaya ya bayyana, mutum yana buƙatar dagewa wajen koyo da kuma kwatantawa har ya kware.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *