Gasar Wasan Kwaikwayo
Gabatarwa
Bakandamiya Reading Club (BRC) ƙungiya ce da ke ƙoƙarin bunƙasa al’adar karatu, rubuce-rubuce, da haɓaka ilimi, tare da fito da basirar matasa a fannin adabi da rayuwa. Tun bayan kafuwar wannan ƙungiya, an gudanar da bukukuwan cikar shekara ta farko da ta biyu cikin nasara, tare da shirye-shiryen ilimi da adabi masu amfani.
Yayin da ƙungiyar ke shirin cika shekara ta uku, an ga dacewar shirya wata gasa ta musamman wadda za ta ƙara ƙarfafa ƙungiyoyin marubuta da matasan marubuta baki ɗaya wajen fito da basirarsu a fagen adabi.
Babbar Manufar Gasar
Babbar manufar wannan gasa ita ce ƙarfafa zumunci da haɗin kai a tsakanin ƙungiyoyin marubuta, tare da inganta rubutun wasan kwaikwayo mai ma’ana, da kuma gano sababbin haziƙan marubuta a fagen adabi.
Manufofin Gasar
- Ƙarfafa matasa wajen rubuce-rubucen adabi
- Haɓaka rubutun wasan kwaikwayo
- Gano sababbin marubuta masu basira
- Bunƙasa manufofin ilimi da adabi na BRC
- Gudanar da bikin cikar shekara uku cikin tsari mai amfani da armashi
Amfanin Gasar
Ana sa ran wannan gasa za ta:
- Ƙara bunƙasa harkokin adabi a cikin al’umma.
- Ƙarfafa marubuta masu tasowa.
- Haɓaka al’adar karatu da rubutu.
- Ƙarfafa haɗin kai tsakanin mambobin ƙungiyoyin marubuta.
- Samar da ingantattun rubuce-rubucen wasan kwaikwayo na Hausa.
Tsarin Gasar
Gasar za ta kasance ta rubutun wasan kwaikwayo mai ma’ana. Masu shiga gasar za su rubuta wasan kwaikwayo wanda:
- Yake ɗauke da jigon illolin ta’addanci a cikin al’umma.
- Yake nuna ƙirƙira da basira.
- Bai gaza fitowa 8 ba.
- Bai wuce fitowa 10 ba.
- Yake da ingantaccen tsari da amfani da harshe yadda ya dace.
- Duk ƙungiyar da aka samu da satar fasaha ko kwaikwayon aikin wani za a cire ta daga gasar.
Wadanda Suka Cancanci Shiga Gasar
Gasar a buɗe take ga dukkan ƙungiyoyin marubuta masu sha’awar shiga, waɗanda za su bi ƙa’idoji da sharuɗan da masu shirya gasar suka gindaya. Ɗaiɗaikun mutane ba za su iya shiga ba. Kowace ƙungiya za ta turo rubutaccen wasan kwaikwayo ta hanyar aiko shi a shafin (website) na BRC.
Kyaututtuka
Na ɗaya = ₦50,000 tare da Satifiket
Na biyu = ₦30,000 tare da Satifiket
Na uku = ₦20,000 tare da Satifiket
- Dukkan satifiket ɗin za su kasance daga Bakandamiya Reading Club ne.
- Dukkan wasannin kwaikwayon da suka yi nasara za a buga su a Bakandamiya Books.
Tsarin Tantancewa
Za a tantance ayyukan masu shiga gasar ne ta la’akari da abubuwa kamar haka:
- Asali da ƙirƙira.
- Ingancin labari.
- Saƙon tarbiyya da ilmantarwa.
- Tsarin fitowa.
- Kyakkyawan amfani da harshe.
- Tasirin wasan kwaikwayo gabaɗaya.
Lokacin Karbar Ayyuka
Za a fara karɓar ayyukan masu shiga gasar daga ranar 3 ga watan Yuli 2026 zuwa ranar 17 ga watan Yuli 2026.
Masu Daukan Nauyi
Kungiyoyi da mutane da dama sun bada gudummawa a wajen shirya wannan gasa. Manya masu daukan nauyi sune:

